IQNA

23:57 - June 14, 2019
Lambar Labari: 3483738
Bangaren kasa da kasa, a zaman kotu da aka gudanar domin sauraren shari’ar Brenton Tarrant da ya kashe musulmi a masallaci, wanda ake tuhumar ya musunta dukkanin abin da ake tuhumarsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, Brenton ya gurfana ne yau juma’a a gaban kotun birnin Aucland na kasar New Zealand, a cikin kwararan matakan tsaro.

A lokacin da lauya mai kare Brenton ya karbi magana a gaban koton, ya ce mutumin da yake wakilta da ake tuhumarsa da aikata aikin ta’addanci ta hanyar kai hari tare da kashe musulmi a cikin masallaci, bai aikata wannan laifin ba.

A cikin watan Maris n Brenton Tarrant dan asain kasar Austraia, ya kai hari kan masallatai guda biyu an musulmi a  garin Christchurch na kasar New Zealand, inda ya kashe musulmi 51, inda kuma ya rika daukar hoton bidiyo da hannunsa a lokacin da yake kisan, daga bisani kuma ya tura a shafukan yanar gizo ba tare da ya boye fuskarsa ba.

Wakilan bangarori da kungiyoyin musulmi 80 ne suka halarci zaman kotun, baya ga daruruwan mutane daga ko’inda daga cikin birnin da suka halarci, domin sauraren shari’ar mutumin da ya aikata wannan ta’asa.

 

3819189

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، New Zealand ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: