IQNA

22:47 - June 16, 2019
Lambar Labari: 3483742
Shugaban Majalisar dokokin Iran ya ce Hukumomin Amurka sun shiga sarkakiyar Siyasa da ta zubar musu da mutunci inda suke sakin kalamai ba tare da sun auna su ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, A yayin jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Shawarar musulinci  ta  Iran a wannan lahadi, Dakta Ali Larijani kakakin Majalisar ya mayar da martani kan fircin baya-bayan nan na saktaren harakokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo inda yake cewa Amukra na amfani da hanyoyin Diplomasiya wajen warware matsalolin  yankin gabas ta tsakiya.

Larijani ya ce ministan harakokin wajen kasar da ta kaddamar da ta'addancin tattalin arziki kan wata kasa da ta bakinsa yake cewa za su ci gaba da tsananta takunkumin tattalin arziki kan Al'ummar wata kasa, shin wannan hanyar Diplomasiya ce.

Ko kuma sayarwa kasar Saudiya makamai da take amfani da su wajen kisan kiyashin da take aiwatarwa kan Al'ummar kasar Yemen? Shin goyon bayan da take bayarwa Sahayuna idon rufe a kan al'ummar Palastinu, shi ma wannan hanyar Demokaradiya ne.

A yayin da yake ishara kan harin da aka kaiwa jiragen dagon man fetir a tekun Oman, Dakta larijani ya ce abinda kasar Amurka ta yi na a matsayin cikon takunkumin tattalin arzikin da ta kakabawa jamhuriyar musulinci ta Iran.

Haka sakamako ne na kasancewar ba ta samu sakamakon da take bukata kan hakan ba, musaman ma idan aka yi la'akari da tarihin Amurka a yakin Duniya, inda ta kusanto da jirgin ruwanta kusa da na kasar Japan sannan ta kai masa hari domin ta hada husuma.

3819706

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: