IQNA

23:49 - June 25, 2019
Lambar Labari: 3483770
Bangaren kasa da kasa, Harkar muslunci a Najeriya ta jadda kira kan a saki Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa da ake tsare da su fiye da shekaru uku a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna,

Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa, a wani taron manema labarai da magoya bayan Harkar muslunci suka gudanar a Abuja, sun kara jaddada kiransu kan a saki Sheikh Zakzaky domin fitar da shi wajen kasar domin yi masa magani.

Abdullahi Muhammad Musa wanda ya yi magana a wurin taron manema labaran ya bayyana cewa, bisa la’akari da cewa tun kafin wannan lokacin kotun tarayya ta bayar da umarnina saki Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa, suna kira ga gwamnatin tarayya da ta saki malamin domin fitar da shi zuwa asibiti a wajen kasar, sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita.

A watannin da suka gabata ne wata tawagar likitoci daga kwamitin kare hakkokin musulmi da ke Birtaniya ta suka ziyarci Sheikh Zakzaky domin duba lafiyarsa, inda suka bayar da rahoton cewa yana fama da matsaloli da ke bukatar duba shi a wajen kasar, inda suka bukaci gwamnatin Najeriya da ta bayar da damar fitar da shi, amma gwamnatin ba ta ce komai kan batun ba.

Daga cikin matsalolin da Sheikh Ibrahim Zakzaky ke fama da su akwai hawan jini, da ke jawo masa shanyewar baren jiki a wasu lokuta, kamar yadda kuma yake fama da matsalar idanu, inda daya daga cikin idanunsa ya mutu baki daya, sakamakon harbin da sojoji suka yi masa, a lokacin da suka kaddamar da farmaki a gidansa a karshen shekara ta dubu biyu da sha biyar.

3822023

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: