IQNA

23:58 - June 25, 2019
Lambar Labari: 3483772
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta ce warware matsalolin tattalin arziki na Falastinawa ba shi ne zai kawo karshen matsalar da ke tsakaninsu da Isra'ila ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna,

kakakin bababn sakataren majalisar dinkin duniya Farhan Haq ya bayyana cewa, matsalar falastinawa ba maganar tattalin arziki ba ce kawai, saboda haka warware matsalarsu ta tattalin arziki ba ya nufin kawo karshen matsalolinsu.

Farhan Haq yana mayar da martani ne dangane da taron da aka fara gudanarwa a kasar Bahrain, da aka kira na saka hannayen jari a Palestine, bayan dage taron yarjejeniyar karni da aka shirya gudanarwa a wanann lokaci.

Ya ce aiwatar da wani shiri wanda zai taimaka falastinawa tare da habbaka tatatlin arzikinsu abu ne mai kyau, amma wannan ba shi ne mafita ta karshe da za ta kawo karshen matsalarsu ba, domin kuwa matsalar falastinawa da Isra’ila magana ce ta makoma ba tattalin arziki ba.

An dai shirya cewa za a gudanar da wannan taro ne a lokacin sanya hannu a kan yarjejeniyar karni tsakanin falastinawa da Isra’ila a zaman na Bahrain, amma ala tilas aka dage taron karni, inda aka maye gurbinsa da taron tatalin arziki kawai, sakamakon matakin da falastinawa suka dauka na kauracewa taron da ma kasashen duniya da dama da aka gayyata.

 

 

3822269

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: