IQNA

23:58 - June 26, 2019
Lambar Labari: 3483775
Bangaren kasa da kasa, Misam Yahya Muhammad 'yar shekaru 6 ita ce yarinya mafi karancin shekaru da ta hardae kur'ani a hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an baiwa Misam lakabin yarinya mafi karancin shekaru da ta hardae kur'ani a hadaddiyar daular larabawa.

Mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa, diyarta mai shekaru shida har yanzu bata zuwa makarata ba, kuma ta fara hardar kur'ani ne tun tana da shekaru uku.

Ta e diyarta ta shiga gasar kur'ani a ta sheikh Zaid kuma ta zo matsayi na bakawai, inda  a ahalin yanzu kuma ta kammala hardar kur'ani baki daya tana da shekaru shida a duniya.

3822455

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: