IQNA

Mahukuntan Saudiyya Sun Hana Wani Dan Najeriya Fita Daga Kasar

22:54 - June 30, 2019
Lambar Labari: 3483793
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Saudiyya sun hana wani dan Najeriya fita daga kasar bayan gurfanar da shi tare da tabbatar da rashin laifinsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jarida Daily Trust ta Najeriya cewa, Alaramma Ibrahim mahardacin kur’ani daga jihar Zamfara, wanda ya tafi aikin umra, amma mahukuntan Saudiyya suka kame shi suka tsare shi.

A zantawarsa da wata kafar yada labarai ya bayyana cewa, ya tafi kasar Saudiyya ne domin gudanar da aikin Umra, kuma gwamnatin Jihar Zamfara ce ta tura shi, amma bayan isarsa jami’an tsaro suka kai masa farmaki a gidan da ya sauka a Jidda.

Ya ce sun ta bincike  agidan bisa zargin cewa yana dauke da miyagun kwayoyi, amma ba su sami komai ba, amma duk da haka sun tafi da shi kuma suka gurfanar da shi a gaban kotun birnin Jidda ba tare da wani dalili ba, bayan da kotu ta kasa samun wani laifi da za ta yi masa hukunci sai ta sallame shi.

Bayan nan kuma ‘yan sandan gwamnatin Saudiyya suka sake cafke suka saka masa ankwa suka kai wata kotu a Makka, a can a aka sake shi, bayan kwashe iye da shekaru biyu a hannun ‘yan sanda, sai mika shi ga ofishin jakadancin Najeriya, amma kuma an hana shi fita daga kasar.

Ya ce yana kira ga shugaba Buhari da ya sa baki a cikin lamarin, domin ba shi dama ya bar kasar Saudiyya domin ya koma ga iyalansa da danginsa a Najeriya.

 

 

3823197

 

 

captcha