Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da yunkurin da magoya bayan harkar musulunci suke yi a Najeriya domin ganin sako jagoran harkar musulucnia kasar Sheikh Zakzaky, a jiya an gudanar da wani jerin gwanoa birnin Abuja fadar mulkin tarayyar Najeriya.
Masu jerin gwanon dai suna rera taken yin kira ga gwamnatin tarayya kan ta saki sheikh Ibrahim zakzaky da ake tsare da shi fiye da shekaru uku da suka gabata, bayan farmakin da sojoji suka kaddamar a gidansa da ke Zaria, inda suka kama shi atre da mai dakinsa, da kuma kashe adadi mai yawa na magoya bayansa.
Wanann jerin gwano na zuwa a daidai lokacin da ake gudanar da irinsa lokaci zuwa lokacia birnin an Abuja, a wasu lokuta hard a wasu daga cikin biranan kasar.