IQNA

23:40 - July 03, 2019
Lambar Labari: 3483805
Bangaren kasa da kasa, gwamnan lardin Sharqiyya akasar Masar ya girmama wasu kananan yara guda biyu yaya da kanarsa da suka hardace kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Mamduh Garrab gwamnan lardin Sharqiyya  akasar Masar ya girmama wasu kananan yara guda biyu ‘yan gida guda da suka hardace kur’ani, masu suna Ahmad da Maryam Ibrahim Dasuqi.

Dukkan yara biyu sun fito ne daga kauyen Aljudaidah da ke karkashin gundumar Minya Kamh a cikin lardin Sharqiyya.

Mamduh Garrab ya girmama wadannan yara tare da ba su lambar yabo ta musamman ta lardin Shaqiyyah.

Gwamnan ya ce hakika wadannan yara sun cancanci girmamawa daga lardin Sharqiyya, domin kuwa suna a matsayin babban abin alfahari ga dukkanin al’ummar wannan , saboda ganin cewa dukkaninsu suna kananan shekaru amma Allah ya yi musu baiwa ta hardar kur’ani mai tsarki.

3824150

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: