IQNA

23:58 - July 06, 2019
Lambar Labari: 3483813
An gudanar da tarukan tunawa da cikar shekaru 37 da sace jami’an diflomasiyyar kasar Iran a kasar a kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya Juma’a an gudanar da taro a birnin Beirut na kasar Lebanon, domin tunawa da cikar shekaru 37 da sace jami’an diflomasiyyar kasar Iran a kasar, wanda wata kungiyar Falanjas ta kiristoci a kasar da take samun goyon bayan Isra’ila ta yi .

An sace mutanen hudu ne a lokacin da Isra’ila take mamaye da kasar Lebanon, uku daga cikin mutanen jami’an diflomasiyyar Iran ne, daya kuma wani dan jirida shi ma dan kasar Iran.

Rahotanin farko sun nuna cewa an kashe mutanen, amma daga baya wasu shaidu sun tabbatar da cewa suna raye kuma suna tsare a hannun Isra’ila, kuma har yanzu Isra’ila taki sakinsu ko kuma yin bayani kan makomarsu.

3824546

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: