IQNA

23:55 - July 07, 2019
Lambar Labari: 3483815
Jikan Nelson Mandela ya caccaki gwamnatin yahudawan Isra’ila kan mulkin wariya a kan Falastinawa.

kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a taron EXPO da aka shirya domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinua  birnin London na kasar Birtaniya, Zwelivelile  Mandela wanda jika ne ga tsohon shugaban Afrika ta kudu marigayi Nelson Mandela, ya bayyana mulkin Isla’ila a matsayin mulkin wariya da kama karya.

Ya ce ko shakka babu suna da masaniya kan irin munin da mulkin wariya yake da shi, domin kuwa al’ummar kasar Afrika ta kudu sun dandana shi a hannun wadanda suka yi mulkin wariyar launin fata a kasar.

Zwelivelile Mandela wanda shi musulmi ne, ya ce babu banbanci tsakanin mulkin wariyar launin fata da aka yi a kasar Afrika ta kudu, da kuma mulkin wariyar da Isra’ila take yi a kan al’ummar Falastinu.

Ya ci gaba da cewa lokaci da al’ummomin duniya za su tsaya a cikin sahu guda wajen kalubalantar danniya da mulkin wariya da ake yi kan al’ummar Falastinu a cikin kasarsu.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake gudanar da taron expo a birnin London na kasar Birtaniya, domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.

 

3825208

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Mande ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: