IQNA

23:50 - July 09, 2019
Lambar Labari: 3483821
Daruruwan jama'a ne suka gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga Sheikh Ibrahim Zakzaky a birnin London an kasar Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya daruruwan mutane sun gudanar da gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga Sheikh Ibrahim Zakzaky a birnin London an kasar Birtaniya, tare da yin kira ga gwamnatin Najeriya kan a sake shi domin nema masa magani.

Wadanda suka gudanar da wanann gangami da jerin ggwanoa  birnin London a yau Litinin, sun hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama da kuma wasu daga cikin kungiyoyin musulmi a kasar.

Kafin hakan dai harkar musulunci ta ce bayannan da ta samu daga likitoci sun tabbatar mata da cewa lafiyar Sheikh Ibrahim Zakzaky ta tabarbare, bayan da aka sami wasu sanadarai masu hatsari a cikin jininsa.

Harkar musulunci a Najeriya a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta tsananta Zanga-zanga ne a cikin kwanakin bayan nan domin yin kira da a sake jagoransu da ake tsare da shi tun a cikin 2015.

3825674

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، zakzaky ، Landan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: