IQNA

23:46 - July 10, 2019
Lambar Labari: 3483825
Jami’an majalisar dinkin duniya mai bincike kan kisan Khashoggi, ta bayyana takaici danagane da yadda duniya ta nuna halin ko in kula dangane da kisan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin wata makala da ta rubuta wadda jaridar Washington Post ta kasar Amurka ta buga, babbar jami’an majalisar dinkin duniya mai gudanar da bincike kan kisan Jamal Khashoggi Agnes Callamard ta bayyana cewa, abin ban takaici matuka, yadda kasashen duniya suka yi gum da bakunansu dangane da kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi.

Ta ce ko shakka babu, kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi bayan ga kasantuwarsa babban aiki ne na laifi mai muni da aka aikata a wuri an aikin diflomasiyya, a lokaci guda guda cin zarafi na dan adam, da kuma murkushe hakkin fadar albarkacin baki.

Ta kara da cewa, da farko bayan faruwar lamarin, wasu ‘yan kadan daga cikin manyan kasashe sun nuna damuwa kamar da gaske, inda har suke yin barazanar daukar matakai na ladabtarwa kan gwamnatin Saudiyya, amma daga bisani ta bayyana cewa wasan kwaikwayo ne suke yi.

A kwanakin baya ne Agnes Callamarda ta fitar da rahotonta na karshe da tawagar bincike ta majalisar dinkind uniya ta fitar kan kisan gillar da aka yi Jamal Khashoggi, inda rahoton ya tabbatar da cewa mahukuntan Saudiyya suna da hannu a cikin wannan laifi, inda ake nuna yatsan tuhuma kai tsaye ga yarima mai jiran gadon sarautar kasar Muhammad Bin Salman kan hakan.

Tun kafin gudanar da bincike daga bangaren majalisar dinkin duniya, hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta sanar da cewa Muhammad Bin salman ne ke da alhakin kisan Jamal Khashoggi, bisa dalilai na musamman da hukumar ta dogara da su, da hakan ya hada da nadir sautin zantuttukan da suka gudana tsakanin Muhammad Bin Salman, da kuma jami’an tsaron Saudiyya da suka aikata wanann kisan gilla jim kadan kafin kisan, da kuma bayan aikata kisan.

Duk da kwararn dalilan da ke akwai da uke tabbatar da wadanda suka aikata wanann mummunan aiki, amma gwamnatin Amurka a tab akin shugabar kasarta Donald Trump, ba za ta taba bata alakarta da gwamnatin Saudiyya ba saboda kisan Khashoggi, domin kuwa tana samun cinikin makaman da daruruwan biliyoyin daloli daga gwamnatin Saudiyya, wanda kuma bata wannan alaka, zai sanya gwamnatin Rasha ta samu wadannan kudade ta hanyar da makamanta ga Saudiyya.

Agnes Callamard ta ce, a halin yanzu dai akwai wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin Amurka da suka hada har wasu ‘yan majalisar dokokin kasar, gami da wasu manyan jami’an jami’an majaliasar dinkin duniya, wadanda suka sha alwashin bin kadun batun kisan Khashoggi da gaske, domin tabbatar da cewa an yi adalci a kan batun kisan gillar da aka yi masa.

 

3825999

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: