IQNA

23:46 - July 11, 2019
Lambar Labari: 3483829
A yau Alhamis za a gudanar da wani gangami a birnin Istanbul na kasar Turkiya, domin yin kira ga gwamnatin Najeriya kan saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wasu kungiyoyin musulmi da na kare hakkin bil adama a kasar Turkiya, sun yi kira zuwa ga gudanar da wani gangami a yau, domin yin kira ga gwamnatin Najeriya, kan ta saki Sheikh zakzaky domin nema masa magani.

Sanarwar hadin gwiwa da bangarorin da suka shiya gudanar da gangami suka fitar ta ambaci cewa, taron gangamin zai fara daga karfe 5:30 na yammacin yau Alhamis a yankin (Eminönü) a gaban sabon babban masallacin birnin Istanbul na Yeni Cami.

Bayanin y ace babbar manufar gangamin ita ce mika kira ga mahkuntan Najeriya, domin daukar matakin gaggawa wajen bayar da dama a fitar da Sheikh Zakzaky domin yi masa magana, sakamakon matsalolin da yake fama da su a inda ake tsare da shi.

Bangarori da dama dai suna ta mika kiraye-kiraye ga mahukuntan najeriya kan wannan batu, kamar yadda ko jiya wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin najeriya sun mika rin wannan kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

 

 

3826132

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: