IQNA

23:48 - July 11, 2019
Lambar Labari: 3483830
Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, ba za su taba fitar da yahudawa daga yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da Kogin Jordan ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yau, firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, dukkanin yahudawa ‘yan share wuri zauna da suke a cikin matsugunnan yahudawa da ke gabar yamma da kogin, ba za su taba fita daga matsugunnan ba.

Ya ce, za su gudanar da wasu shirye-shirye na tattaunawa domin cimma matsaya kan makomar yankunan gabar yamma kogin Jordan, domin samun daidaito tsakanin Isra’ila da Falastinawa kan yankunan, amma Isra’ila ba za ta taba amincewa da duk wani batun ficewar yahudawa daga yankin ba.

Netanyahu ya kara da cewa, yanzu haka suna kokarin ganin sun gaba da kara fada ayyukansu na ci gaba da gina wasu sabbin matsugunnan yahudawa a cikin yankunan gabar gabar yamma da kogin Jordan, domin kuwa a cewarsa yankunan Isra’ila ne.

3826256

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kamfanin dillancin labaran iqna ، iqna ، netanyahu ، isra’ila
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: