IQNA

22:49 - July 13, 2019
Lambar Labari: 3483835
Bangaren kasa da kasa, kasashe 35 na gyon bayan irin matakan cin zarafin musulmi da gwamnatin China take dauka daga cikin kuwa har da wasu kasashen musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Russia today ta bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin kasashe sun goyi bayan matakan da China take dauka a kan musulmin yankin Igor, da suka hada da Rasha, Belarus, Koriya ta arewa, Cuba, Venezuela, Myanmar, Pakistan, Philipines, da kuam wasu kasashen larabawa da suka hada da Syria, Kuwait, Oman, Qatar, UAE, Bahrain.

Wadannan kasashe sun nuna cewa abin da China take yaki ne da tsatsauran ra’ayi, wanda kuma yana matsayin yaki da ta’addanci.

Kafin wannan lokacin dai China ta bayyana cewa akwai ‘yan kabilar Igor wadanda akasarinsu musulmi ne da suke samun akidu da ke saka su cikin ayyukan ta’addanci, inda wasu daga cikinsu sn shiga kungiyoyin ta’addanci da ke yakia  aSyria da Iraki da sauransu.

Majalisar dinkin duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama na dniya suna ganin matakan da China take dauka sun yi tsauri, musamman ma yadda take yin hukunci a kan dukkanin musulmin yankin, da cewa suna mara baa ga ta’addanci.

3826593

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: