IQNA

22:49 - July 14, 2019
Lambar Labari: 3483838
Wani mai fafutuka a kasar Afrika ta kudu ya bayyana shirin saudiyya na gudanar da babban taron rawa da cewa cin zarafin muslucni da musulmi ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Muhammad said wani musulmi mai fafutuka  akasar Afrika ta kudu, ya bayyana cewa shirin da gwamnatin saudoyya take da shi na shirya wani taro na wakoki da raye-raye a ranar 18 ga Yuli da hakan babban cin fuska ne ga dukkanin musulmin duniya.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin saudiyya ta shirya wannan babban taron raye-raye da badala ne a daidai lokacin tuni maniyyata musulmi daga dukkanin kasashen duniya suka fara isa kasar domin gudanar da aikin hajji.

Baya ga haka kuma wannan wata wata ne mai alfarma na zulkida wanda wata ne da ake lissafa shi a matsayin watan shirin aikin hajji, wanda tozarta wannan wata yana matsayin tozarta aikin hajji, da ma alhazai da suke isa kasar a halin yanzu.

Yariman saudiyya ya shirya wannan taron kide-kide da raye-raye ne da sunan yana son jawo hankulan masu saka hannayen jari daga kasashen waje musamamn na turawa.

3826660

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، gudanar ، lissafa ، hajji
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: