IQNA

21:49 - July 16, 2019
Lambar Labari: 3483845
Bangaren kasa da kasa, gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida ta kasar Jordan ta yi kira da a ladabtar da tashar talabijin da ta tozarta mahardata kur’ani a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a jiya gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida a kasar Jordan ta yi kira da a dauki matakin ladabtar da tashar talabijin din da ta tozarta addini ta hanyar cin zarafin mahardata kur’ani mai tsarki.

A cikin bayanin da kungiyar ta fitar ta bayan yin Allawadai da kakakusar murya, ta bayyana cewa addinin muslunci a wurin dukkanin musulmi yana gaba da komai, saboda haka ba abu ne da za a lamunta da shi ba wani bangare na watsa labarai yak eta hurumin muslunci a Jordan.

Daga karshe kungiyar ‘yan jaridun ta kasar Jordan ta yi da a dauki matakin bin kadun wannan lamari, domin hukunta dukkanin wadanda suke da hannu wajen watsa shirin da ya ci zarafin kur’ani.

3827721

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Jordan ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: