IQNA

21:53 - July 16, 2019
Lambar Labari: 3483846
Bangaren kasa da kasa, ‘yan majalisar dokokin Amurka mata hudu ad Trump ya ci wa zarafi sun mayar masa da martani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa,’yan majlaisar dokokin Amurka mata Alexandria Ocasio-Cortez, Ilhan Omar, Rashida Tlaib, and Ayanna Pressley, sun bayyana cin zarafin da Trump ya yi musu da cewa yana neman dauke hankulan jama’a ne daga barnar da gwamnatinsa ke tafkawa.

Pressley daya ce daga cikin ‘yan majalisan wadanda Trump ya ci wa zarafi, ta bayyana cewa tana kira ga Amurka da kada su mayar da hankali ga kalaman Trump, domin kuwa yana son ya kawar da hankulan su ne daga abin da ke faruwa a gwamnatinsa, domin kada ya fuskanci matsala a lokacin zabe.

A cikin bayanan da ya watsa a shafinsa na twitter, Trump ya bayyana wadannan ‘yan majalisar dokoki wadanda dukakninsu Amurka ne da aka Haifa a cikin kasar in banda Ihan Omar, da cewa ba ‘yan kasar Amurka ba ne bakin haure ne, ku su koma inda suka fito.

Wadanann kalamai na cin zarafi da nuna wariya da kyama na Donald Trump a kan Amurka ‘yan kasarsa, na ci gaba da fuskantar kakkausar daga ciki da wajen kasar.

 

3468974

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Amurka ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: