IQNA

23:57 - July 18, 2019
Lambar Labari: 3483855
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin 'yan jam'iyyar Labour a Birtaniya sun zargi Jeremy Corbyn da yada kiyayya ga yahudawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar Labour babbar jam’iyyar adawa a kasar Birtanitaniya, sun zargi shugaban jam’iyyar Jeremy Corbyn da nuna kiyayya ga yahudawa.

Kamfanin dillancin labaran Reauters ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin kasar Birtaniya ‘yan jam’iyyar adawa da Labour, sun sanya hannu kan wata takarda, wadda take zargin shugaban jam’iyyar Jeremy Corbyn da nuna adawa ga Isra’ila.

Sai daianata bangaren uwar jam’iyyar ta kasa ta kore zargin da ake yi kan Jeremy Corbyn na yada kiyayya a kan Isra’ila a cikin jam’iyyar ta Labour da kuma cikin al’umar Birtaniya.

Corbyn dai ya shahara da nuna cikakken goyon baya ga al’ummar falastinu, da nuna rashin yarda da salon siyasar zalunci ta Isra’ila a kan al’ummar falastine, matakin da mahukuntan Birtaniya suke nuna damuwa a kansa.

Baya ga haka kuma matakin da ya dauka na nuna goyon bayan baya ga kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa musamamn hamas, da kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, wannan ya kara tunzura masu adawa da shi wajen kokarin ganin an dakushe tasirinsa a siyasance akasar Birtaniya.

3827983

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: