IQNA

23:46 - July 19, 2019
Lambar Labari: 3483856
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, Amurka ba za ta iya kaddamar da yaki kan kasar Iran ba saboda dalilai da dama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta ewa, a ganawar da ta gudana tsakanin babban sakataren kungiyar Hizbullah Syyid Hassan Nasrollah da kuma mataimaki na usamman ga shugaban maalisar dokokin Iran Amir Abdollahian, Sayyid Nasrollah ya bayyana cewa, Amurka ba za ta iya yin gigin kaddamar da hari kan kasar Iran a wannan lokaci ba.

Sayyid Nasrolah ya ce babban dalilin da yasa Amurka ba za ta yi gigin yin hakan ba, saboda tafi kowa sanin cewa, idan ta bude yaki da Iran, to kuwa ba yaki ne da zai tsaya kan kasar Iran, zai game gabas ta tsakiya ne, wanda kuma hakan zai yi babbar illa ga ita kanta Amurka.

Dangane da batun Palestine kuwa, Sayyid Nasrollah ya bayyana cewa, babu yadda za a yi adalci ga al’ummar falastinu matukar ba a kafa kasar falastinu mai cin gishin kanta ba a hukumace, ku haka ba zai yiwu ba har sai agudanar da kuri’ar raba gardama tsakanin dukkanin ‘yan asalin falastine, da suka hada da musulmi, larabawa kiristoci da yahudawa.

Dangane da batun abin da ake kira da yarjejeniyar karni kuwa, ya bayyana hakan a matsayin wani babban ha’inci ga al’ummar falastinu da musulmi da larabawa baki daya.

A jiya ne, mataimin na musamman ga shugaban majlaisar dokokin Iran Air Abdollahian ya ziyarci Sayyid Nasrollah, a ziyarar da ya kai kasar Lebanon.

 

3828309

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Nasrollah ، Iran ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: