IQNA

23:51 - July 22, 2019
Lambar Labari: 3483868
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaro sun yi amfani da harsasan bindiga akan masu gudanar da jerin gwano na kira da a sai Sheikh Zakzakya Abuja.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, jami’an tsaron sun fara harbi akan masu Zanga-zangar a kusa da ginin sakateriyar gwmanatin tarayya dake birnin Abuja.

Majiyar harkar musulunci a Najeriya ta ambaci cewa; daga cikin wadanda aka harba din da akwai kananan yara da mata.

Tun bayan da aka fitar da wani rahoto na likitanci dake cewa lafiyar shugaban harkar musuluncin ta Iran ta kara tabarbarewa, mabiyansa suke gudanar da Zanga-zangar yin kira da a sake shi domin neman magani.

3829246

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: