IQNA

23:43 - July 23, 2019
Lambar Labari: 3483870
Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, suna yin kira ga gwamnatin Najeriya kan ta bayar da dama domin sama ma sheikh Ibrahim magani a asibitocin da suka dace.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sayyid Abbas Nusawi a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Tehran, ya bayyana cewa, suna kara jaddada kira ga gwamnatin Najeriya kan ta duba batun Sheikh Zakzaky, musamman halin rashin lafiyarsa.

Ya ce bisa la’akari da cewa yanayin da yake ciki yana da matukar hadari, mahukuntan Najeriya za su iya yin abin da ya kamata na bayar da dama a fitar da shi domin kula da lafiyarsa da ke ci gaba da kara tabarbarewa.

Dagane da abin da ya faru a ranar Litinin a birinin Abuja kuwa, Musawi ya bayyana cewa abin da ya faru ba mai faranta rai ba ne.

Ya suna fatan ganin an samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a Najeriya, kamar yadda kuma suke fatan ganin gwamnatin kasar ta dauki matakin sauraren kiraye-kirayen da magoya bayan Sheikh zakzaky suke yin a neman a bayar da damar fitar da shi domin kula da lafiyarsa.

3829368

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: