IQNA

matsayar Jagora Kan Kisan Matasa Biyu A Bahrain

22:59 - July 31, 2019
Lambar Labari: 3483897
Bangaren siyasa Ofishin jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Iran ya bayana matsayar jagora kan kisan da gwamnatin Baharai ta yiwa matasa biyu a cikin yan kwanakin nan.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin jagoran ya bayyana martanin jagora kan wannan ta'addanci inda ya ce jagoran juyin juya halin musulinci ya ce zalunci da amfani da karfi ba zai dawwama ba, abinda al'umma ke so na tabbatar da adalci ba da jimawaba zai tabbata.

A ci gaba da farmakin da gwamnatin Ali-khalifa ta kasar Bahren ke kaiwa 'yan adawa, a ranar asabar din da ta gabata ce ta zartar da hukuncin kisa kan wasu matasan kasar biyu, Ahmad Malaali mai shekaru 24 da kuma Ali Al-arab mai shekaru 25 bayan azabtar da su.

A baya dai jagoran juyin juya halin musulinci ya sha mayar da martani na yin tir da irin ta'addancin da masarautar Ali- khalifa ke aiwatarwa kan 'yan adawar kasar.

 

3831574

 

 

 

captcha