IQNA

23:55 - August 07, 2019
Lambar Labari: 3483923
Bangaren kasa da kasa, mataimakin shugaban kwamitin tsaro a majalisar Doma a Rasha ya mayar da martani kan rahoton yaduwar Daesh a Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, Yuri Shcotin mataimakin shugaban majalisar Doma ta kasar Rasha, ya bayyana cewa Amurka na da wata manufa dangane da rahoton da ta fitar, kan sake dawowar daesh a  Syria a wanann lokaci.

Ya ce kasarsa ba ta da wata matsala a Syria, kuma bat a da wata bukatar kara yawan dakarunta  a kasar a halin yanzu, idan kuma akwai bukatar hakan za ta kara ba tare da la’akari da rahoton Amurka ba, domin kuwa dakarun Rasha suna zaune nea  Syria bisa izinin gwamnatin kasar.

A cikin wanann makon ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka Pentagon ta fitar da rahoto, da ke cewa; a cikin yan lkutan nan Daesh tana wasu shirye-shirye domin sake dawowa a cikin Syria, rahoton da Rasha ke kallon cewa Amurka tana wata da wata manufa kan hakan a kan kasar ta Syria.

 

3833422

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Rasha ، Pentagon ، Daesh
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: