IQNA

23:59 - August 07, 2019
1
Lambar Labari: 3483924
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta nuna damuwa kan batun Soke kwarkwaryan cin Gishin Kashmir ta India

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin bayanin da kungiyar ta OIC ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta bayyana yanayin da ake ciki a yankin na Keshmir da cewa yana da matukar hadari, kuma yana daga hankali matuka.

Bayanin ya ce; kungiyar ta OIC tana kiran dukkanin bangarori, da suka hada da mahukuntan India da kuma jagororin al’ummar yankin Keshmir, da su zauna kan teburin tattaunawa domin warware matsalolinsu ta hanyar fahimtar juna.

Haka nan kuma OIC ta kirayi India ta mutunta kaidoji na kasa da kasa, musamamn wadanda majalisar dinkin duniya ta amince das u kan batun yankin Keshmir.

A ranar Litinin da ta gabata ce gwamnatin kasar India ta sanar da cewa ta kawo karshen kwarya-kwaryan cin gishin kai da yankin Keshmir yake da shi, lamarin da ya fusata kasar Pakistan ta sanar da yanke alakarta da kasar India.

3833286

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Kasmir ، India
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
suraka
0
0
Allah samudace
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: