IQNA

22:50 - August 11, 2019
Lambar Labari: 3483935
Bangaren kasa da kasa, a yau ne maniyyata suka fara gudanar da jifar shedan ta farko a Mina.

Bayan tsayuwar arfa da ta gudana a jiya Asabar mahajjata suka isa Mina, inda suka fara ibadar jifar shaidan a safiyar yau, sannan daga bisani suka yanka dabbobinsu, da kuma yin aski wanda hakan ya ba su damar sauke haraminsu, inda mahajjatan suka koma Makka domin yin dawafi sannan kuma su sake komawa filin Mina su ci gaba da zama na cika ayyukan aikin hajji.

A gobe Lahadi ne mahajjatan za su yi jifar shaidan na biyu, sannan kuma su kasance a Mina har zuwa marecen ranar Talata bayan jifar shaidan karo na uku za su kammala ayyukansu na hajji, inda za su koma Makka, inda daga nan ne kuma za a fara shirye-shiryen komawa gida.

Aikin Hajji dai nadaya daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da yake a matsayin wajibi a kan kowane musulmi mai hali.

Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga watan Zul Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan.

A kowace shekara miliyoyin musulmi ne daga kasasheh duniya daban-daban ke gudanar da aikin Hajji abirnin Makka mai alfarma.

 

3834150

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Mina ، aikin hajji
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: