IQNA

Iran Ba Za Ta Yi Kasa A Gwiwa Kan Hakkokin Al'ummomi Ba

22:53 - August 11, 2019
Lambar Labari: 3483936
Shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran ya bukaci kasashen Indiya da Pakistan su kai zuciya nesa domin kauce wabarkewar rikici da kuma kare rayukan fararen hula a yankin Kashmir.

A yayin da yake tattaunawa da Firaministan kasar Pakistan Imran Khan ta wayar tarho a wannan Lahadi, shugaban kasar Iran dakta Hasan Rouhani ya bayyana muhimancin zaman lafiya a yankin, sannan ya ce jamhuriyar musulinci ta Iran ba za ta taba da ja da baya domin ganin an tabbatar da da tsaro da sulhu a yankin da kuma tabbatar da hakkin al'ummar musulmi ba.

Shugaba Rouhani ya yi ishara da cewa kasashen Iran da Pakistan makwabtan juna ne kuma 'yan uwa da aminan juna ne a kowane lokaci, ya ce kasar Iran tana kokarin ganin shiga gaba, domin hana barkewar rikici da tashin hankali a yankin, amma wajibi ne al'ummar musulmi na yankin Kashmir su kare hakkokinsu ta yadda za su yi rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Shugaba Rouhani ya kara da cewa rikicin yankin Kashmir ta hanyoyi na diflomasiyya da tattaunawa da kuma fahimtar juna tsakanin dukkanin bangarori ne kawai za a iya warware rikicin yankin Kashmir.

A nasa bangare Firaministan kasar Pakistan Imran Khan ya bayyana alakar dake tsakanin kasarsa da Iran da cewa ta ‘yan uwantaka ce, sannan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka kashe fararen hula da ba su ji ba su gani ba a yankin na Kashmir ,sannan ya ce jamhuriyar musulinci ta Iran dake a matsayin kasa mai muhimanci a yankin da ma Duniyar musulmi za ta iya taka muhimiyar rawa wajen warware rikicin yankin na Kashamir.

A ranar Litinin din da ta gabata ce kasar Indiya ta jingine kwarya-kwaryar cin gashin kai da kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar wa Yankin na Kashmir.

Al'ummar Kashmir dai sun bukaci zartar da kudirin kwamitin tsaron Majalisar Dindin Duniya na gudanar da zaben raba gardama na al'ummar yankin, sai dai gwamnati kasar Indiya ta nuna adawar da shi.

3834225

 

captcha