IQNA

22:58 - August 15, 2019
1
Lambar Labari: 3483951
Bangaren kasa da kasa, shugaban cibiyar kusanto da mazhabobin mulsunci Ayatollah Mohsen Araki ya zanta da Sheikh Zakzaky ta wayar tarho.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a yayin zantawar, sheikh Zakzaky ya sheda wa Ayatollah Araki cewa har yanzu ba a fara yi masa magani ba, saboda wasu matsaloli da aka samu, sakamakon rashin bayar da cikakken bayani ga asibitin da take daukar nauyin jinyarsu tare da mai dakinsa.

A nasa bangaren Ayatollah Araki ya bayyana fatan ganin an samu nasara wajen gudanar da dukkanin ayyukan da ake sa ran za a yi wa sheikh Zakzaky da kuma mai dakinsa a kasar ta India.

Sheikh Zakzaky ya fitar da sakonni daga asibitin da yake a kasar India, inda yake yin korafi kan rashin aiwatar da abin da aka yi magana a kansa tun daga Najeriya, inda ya bayyana cewa; likitocin asibitin sun bayyana masa cewa za su fara aikin ne tun daga farko domin gano abin da ke damunsa, alhali tuni likitocin da suka duba shi daga Birtaniya har sun fitar da sakamakon gwaje-gwajen da suka yi kan matsalolinsa, wanda bisa hakan ne kotu ta amince domin fitarsa zuwa wajen kasar domin neman magani.

Baya ga haka kuma Sheikh Zakzaky ya yi korafi kana bin da ya kira matakan takura masa da ake dauka a asibitin, ta hanyar saka masa masu gadi a bakin kofa da bindigogi.

Sai a nata bangaren gwamnatin tarayyar Najeriya, kamar yadda kamfanin dillancin NAN na gwamnatin Najeriya ya nakalto, gwamnati ta bayyana cewa sheikh Zakzaky ya nemi kawo matsala ne dangane batun tafiyar tasa.

Rahoton yace, jami’an gwamnatin sun ce tun daga Dubai ne ya bukaci da a mika masa fasfo nasa, kuma a kasar India a kama masa katafaren otel, abin da gwamnatin take ganin cewa hakan na a matsayin wani abu ne na neman kawo tarnaki a tafiyar.

 

3835105

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
MUHD INUWA ISAH
0
0
ALLAH YANA BAYAN ME GASKIYA IN SHA ALLAHU
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: