IQNA

23:49 - August 21, 2019
Lambar Labari: 3483972
Bangaren kasa da kasa, musulmi ahlu sunna da dama ne suka halarci tarukan Ghadir da aka gudanar a birane daban-daban na kasar Bosnia.

Kamfanin dillanicn labaran iqna, musulmi ahlu sunna da dama ne suka halarci tarukan da aka gudana na Ghadir a biranen Sarayevo, Visoko da Traunik da sauransua  kasar Bornia.

Wadanda suka gabatar da bayanai a wuraren tarukan sun mayar da hankali ne dangane da matsayin wannan rana da kuma gagarumin lamarin da ya faru a cikinta, wada yake a matsayin cikon addini.

Taron Ghadir na wannan shekara  akasar Bosnia ya dauki sabon salo da ba a saba gani ba, inda mabiyar mazhabar ahlul bait ne suka saba halartar wannan taro, amma a shekarar bana har da ahlu sunna.

Wannan lamari ya nuni da cewa batun Ghadir ba na wani bangare ba ne na musulmi, lamari na dukkanin al'ummar musulmi baki daya.

 

3836672

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: