IQNA

23:52 - August 21, 2019
Lambar Labari: 3483973
Bangaren kasa da kasa, an bude makarantar kur'ani ta farko ta kurame mata a kasar Masar baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, an bude makarantar farko ta mata kurame ta koyar da kur'ani mai tsarki a lardin Minya na kasar Masar.

Wannan dai ita ce makarantar farko wadda aka bude wadda za ta rika koyar da mata kurame karatun kur'ani mai tsarki ta hanyar harshen ishara, wanda ya samu karbuwa daga sassa daban-daban na al'ummar kasar.

A halin yanzu dai an sanar da tsare-tsaren makarantar da kuma abubuwan da za a koyar, wanda hakan ya hada da karatun kur'anin da kuma wasu ilmomi da suka hada na fikihu da sauransu.

Sheikh Allamah Abdulrazzaq wakilin ma'aikatar kula da harkokin addini a yankin shi ne ya jagoranci bude makarantar.

3836471

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، kurame ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: