IQNA

Iran Za Ta Yi Amfani Da Hanyoyi Na Shari'a Domin Kare 'Yan Kasarta

23:52 - August 27, 2019
Lambar Labari: 3483992
Bangaren siyasa, Iran za ta yi amfani da hanyoyi na doka domin kalubalantar dokar FDD ta Amurka a kan Iran da harkokinta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Sayyid Abbas Musawi kakakin  ma’aikatar harkokin wajen Iran a  lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da doka Amurka ta kakaba takunkumi kan wasu kaddarorin kasar Iran a kasashen ketare, ya bayyana cewa wannan doka ta Amurka mai suna FDD ba sabon abu ba ne, domin kuwa tun kafin wanan lokacin Amurka ta saba sharara karya a kan Iran domin ta samu hujjar cutar da Iran.

Ya ce kasarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare dukkanin abin da yake maslha a gare ta, kamar yadda kuma za ta ‘yar kasarta a duk inda suke a duniya, tare da daukar matakai na doka domin hakkokinsua  duk inda a ka cutar da su da sunana takunkumin Amurka.

Daga karshe ya kirayi hukumomin Amurka da su fifita yin amfani da hankali da kuma kaida da kiyaye dokoki na kasa da kasa, mai makon yin hawan kawara a kansu a lokacin da take dawa’ar kiyaye doka da kuma neman wasu su bi doka da kuma kiyaye ta.

 

3837450

 

captcha