IQNA

23:34 - August 31, 2019
Lambar Labari: 3484003
Bangaren kasa da kasa, tsohon shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya sake bayyana a gaban kotu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tsohon shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan al-Bashir wanda ya sake bayyana a gaban kotu a yau Asabar domin amsa tambayoyi akan tuhumar da ake yi masa ta sama da fadi da kudade, ya sake bayyana kudaden da ya karba daga yarima mai jiran gado na Saudiyya.
An tsaurara matakan tsaro a kotun a yayin da ake shari’ar hambararren shugaban kasar ta Sudan, haka nan kuma an rufe muhimman hanyoyin da suke isa gare ta.
Alkalin da ya jagoranci zaman kotun, as-Sadiq Abdurrahma al-faky, ya saurari bayanan da su ka fito daga Umar Hassan al-Bashir a karon farko, kuma ya yi watsi da bukatar lauya mai ba da kariya akan bayar da bellin tsohon shugaban kasar.
Al-Bashir ya ce; Ya karbi kudade wuri na gugar wuri har dalar Amurka miliyan 25 daga Yarima mai jiran gado na Saudiyya, muhammadu Bin Salman, ta hannun shugaban ofishinsa Hatim Hassan Bukhait.
Al-Bashiry ya ci gabada cewa; Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya aike da kudin ne ta hanyar jirgin sama na musamman wanda Bukhait ya tarba.
Bugu da kari al-Bashir ya ce; babu wani zabi da muke da shi da ya wuce mu karbi kudin kai tsaye, ko kuma mu mayar da su,amma mun zabi karBa ne domin mayar da su ba zai yi wa yariman na Saudiyya dadi ba.

 

3838907

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: