IQNA

17:34 - September 09, 2019
Lambar Labari: 3484032
An gudanar da zaman juyayi a ranar Tasu’a Hussainiyar Imam Khomaini da ke Tehran.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da zaman taron juyayi  na ranar Tasu’a a Husainiyar Iamm khomeni da ke birnin Tehran, tare da halartar jagoran juyin juya halin muslucni a Iran, da kuma sauran jami’a gami da al’ummar gari.

A yayin wannan taro dai malamai sun gabatar da jawabai kan matsayin wannan rana da kuma abubuwan da suka faru a ranar Tasu’a wadda ita ce ranar da aka tsananta killace iyalan gidan manzon Allah a karbala, da nufin yi musu kisan gilla kamar yadda ya tabbata a tarihi.

Aghaye Ali wani malami da ya gabtar da jawabi a wurin, ya yi ishara zuwa ga irin darussan da suke a  cikin wannan waki’a mai girma  a cikin addinin muslunci.

Kamar yadda wasu malam da suka gabatar da nasu jawaban, suka tabo muhimamn abubuwan da suka farua  wanann rana bisa dogaro da sahihan ruwayoyi na tarihi.

 

3841110

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: