IQNA

17:36 - September 09, 2019
Lambar Labari: 3484033
Ministar harkokin wajen kasar Sudan ta bayyana cewa yanzu ba lokaci na bijiro da maganar kulla alaka da Isra’ila ba.

A lokacin da take zanatwa da tashar Aljazeera a jiya, Asma’u Muhammad Abdullah ministar harkokin wajen kasar Sudan ta bayyana cewa, yanzu ba lokaci ne da ya dace a dauko batun kulla alaka tsakanin Sudan da Isra’ila ba.

Ta ce akwai abubuwa wadanda suke da muhimamnci a gaban kasar Sudan a halin yanzu, amma duk da haka batun kulla alaka da sauran kasashe na daga cikin abubuwa masu muhimamnci da ke gaban  kasar.

Ta kara cewa, kulla alaka da kuma kyautata tsakanin Sudan da kasashen larabawa da kuam kasashen Afirka shi ne yafi komai muhimmanci ga Sudan dangane da batun alaka tsakaninta da kasashen ketare.

Haka nan kuma ta yi ishara da batun takunkuman da Amurka da kakaba wa kasar, da kuma muhimamncin cire wadannan takunkumai, da kuma cire sunan Sudan daga cikin jerin sunayen da Amurka ta kira masu daukar nauyin ta’addanci.

A jiya ne gwamnatin Sudan karkashin jagorancin sabon Firayi minister Abdullah Hamduk ta sha rantsuwar kama aiki tare da halartar dukkanin sabbin ministocin gwamnatin.

An kafa gwamnatin rikon kwarya a Sudan ne bayan cimam matsaya tsakanin bangarorin siyasa da farar hula da kuma sojojia  daya bangaren, kan kafa gwanmati wadda za ta hada dukaknin bangarori.

3841201

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bangarori ، siyasa ، Hamduk
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: