IQNA

22:55 - September 12, 2019
Lambar Labari: 3484042
Bangaren kasa da kasa, an kammala gasar karatun kur’ani mai tsarki ta duniya akasar saudiyya inda dan Falastinu ya zo na uku.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa, a yau ne aka kawo karshe gasar karatun kur’ani mai tsarki ta duniya  a kasar saudiyya inda dan Falastinu Musa Muhammad Midfa ya zo na uku a wannan gasa.

Haka nan kuma an fitar mutane 12 ne daga cikin masu gasar da suka fi nuna kwazo kuma aka ba su kyautuka na musamman bayan kyautuka na bai daya da aka bayar ga dukkanin wadanda suka halrci wannan gasa.

Musa MuhammadMidfa daga Falastinu ya nuna kwazo maktuka inda ya zo matsayi a hardar dukkanin kur'ani mai tsarki, yayin Mujahid Bin Faisal Awad Al-radadi daga kasar saudiyya ya zo na daya.

Hisab Abu al-rab wakilin ma'iakatar kula da harkokin addinin falastinu da ya haarci wannan gasa ya nuna farin cikinsa matuka dangane da irin kwazon da wakilin falastine ya nuna a wannan gasa.

Wannan dai shi ne karo na 41 da ake gudanar da wannan gasa a kasar Saudiyya, a wannan karon an gudanar da gasar a bangarori biyar ne.

 

3841723

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: