IQNA

23:00 - September 12, 2019
Lambar Labari: 3484043
Bangaren kasa da kasa, Zahiri ya kirayi mabiyansa da su akiwa Amurka da Isra'ila hari.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Sedaye Afghan cewa, a jiya Aiman Zawahiri, jagoran kungiyar Alka’ida ya fitar da wani bayani ga mabiyansa, dangane da ci gaba da kai hare-harensu a kan wadanda ya kira makiya.

A cikin bayanin nasa Zawahiri ya bayyana cewa, suna na kan bakansu na yin abin da ya kira da jihadi, kuma barazanar Amurka ba za ta karya musu gwiwa ba, inda yace hare-harensu  za su hada kasashen Amurka, Isra’ila, Faransa, Birtaniya, Rasha da kuma sauran kasashen turai.

Tun bayan kisan jagoran kungiyar Alkaida Osama Bin laden, Zawahiri bababn na hannun damarsa ya zama jagoran kungiyar, inda yake ci gaba da harkokinsa a boye ba tare da sanin inda yake ba.

Kungiyar Alkaida dai ta dauki alhakin hare-haren ta’addancin 11 ga watan Satumba a kasar Amurka, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 3000, da suka hada da Amurkawa da ma wadanda ba Amurkawa, da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

3841710

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: