IQNA

23:17 - September 13, 2019
Lambar Labari: 3484046
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da gasar kur’ani ta Share fage ta dalibai ‘yan shekaru 12 zuwa 18 a Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na QAF cewa, ana shirin fara gudanar da gasar Share fage ta kur’ani a kasar Iraki bai daya.

Rahoton ya ce wannan gasa dai za ta kasance ta dalibai ce zalla wadanda suka hada da ‘yan aji daya na sakadandare har zuwa wadanda za su kammala karatunsu na sakandare.

Bangaren kula da harkokin kur’ani na ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Iraki ne zai dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan gasa kama yadda aka saba yi a kowace shekara.

Gasar dai za ta hada dukkanin daibai ne na dukkanin makarantun sakandare na kasar Iraki baki daya, kamar yadda kuma za a raba bangarorin mata da maza.

Yanzu haka dai an bayyana sharudda da ake bukata daga masu son shiga gasar, da suka hada da harda da kuma iya karatun kur’ani da sanin ka’idojin karatun yadda ya kamata.

3841798

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: