IQNA

23:41 - September 20, 2019
Lambar Labari: 3484070
Kakakin magatakardan UN yace Antonio Guterres ya jaddada wajabcin tattauna kan matsalar Kashmir.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamafanin dillancin lababar Associated Press ya bayar da rahoton cewa, maimagana da yawun babban sakataren majalisar dinkin Stefan Dujarick yace Antonio Guterres ya jaddada wajabcin tattauna kan matsalar Kashmir da take ta’azzara.

Ya ce zaman babban zauren majalisar dinkin duniya babbar dama ce ga dukkanin bangarorin da abin ya shafa domin tattaunawa, da kuma samo hanyoyin warwae wannan matsala.

Ya ci gaba da cewa, yana shirin kiran wani zama kan batun na Kashmir wanda zai hana bangarori daban-daban a zaman bababn zauren majalisar dinkin duniya, kuma yana fatan hakan ya haifar da da mai ido ga dukkanin bangarorin.

Tuna  cikin watan da ya gabata ne dai gwamnatin India ta soke dokar da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar mai lamba 370, wadda ta baiwa yankin Kashmir na India kwarkwaryan cin gishin kai.

 

 

3843384

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: