IQNA

23:03 - September 21, 2019
Lambar Labari: 3484073
Al ummar kasa Masar na gudanar da jerin gwanon neman Sisi ya sauka daga shugabancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, rahoanni dake fitowa daga birnin Alkahira sun bayyana cewa Daruruwan mutane ne suka bazama akan titunan suna gudanar da zanga zangar neman shugaban kasar Abdulfatah Alsisi ya yi murabus daga shugabancin kasar inda suke tar ere takin dake zargin gwamnatin da cin hanci da rashawa.
Tuni jami’an tsaro suka daukar matakin tarwatsa masu zanga zangar ta nayar harba musu hayaki mai sa hawaye a inda masu zanga zangar suka taru ,sai dai wata majiya ta nuna cewa matasan sun hau kan tituna suna ta rera taken cewa Sisi ya ya fi,
Yanzu haka dai an dauki tsauraran matakantsaro a dandalin Tahrir dake birnin na ALkahira wajen da dubban masu zanga zanga suka taru a shekara ta dubu biyu da sha daya har suka kada gwamnatin tsohon shugaban kasar Husni Mubarak.

 

3843492

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، Alsisi ، zanga-zanga
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: