IQNA

22:23 - September 22, 2019
Lambar Labari: 3484075

Rauhani: Mu Masu Son Sulhu Da Zaman Lafiya Ne Masu Kare Kai Idan An Tsokane Mu

Shugaba Rauhani na Iran  ya gabatar da wani jawabia  yau a wurin taron ranar farko ta makon tsaron kasa a Iran.

Rauhani: Mu Masu Son Sulhu Da Zaman Lafiya Ne Masu Kare Kai Idan An Tsokane Mu

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya kudiri anniyar gabatar da wani shiri kan tsaro a yankin Golf da zai shafi, mashigar ruwa ta Hormoz da kuma tekun Oman a gaban babban zauren taron MDD da za’a faraway a makon gobe.

Dakta Rohani, na bayyana hakan ne, a cikin jawabin da ya gabatar yau, yayin da yake halartar bikin faretin sojojin kasar na zagayowar cika shekaru 39 na makon tsaron kasa.

A cikin jawabin da ya gabatar tun daga hubaren mirigayi Imam Khomaini, wanda ya asasa jamhuriya musulinci ta Iran, shugaba Rohanin, ya yi alkawarin cewa a cikin kwanaki masu zuwa gaban taron koli na MDD, zai gabatar da wani shiri na karfafa tsaro a yankin, golf da mashigar Hormuz da kuma tekun Oman, wanda a cewarsa kasancewar dakarun ketare a yankin zai iya kasancewa barazana ga tsaron harkokin mai da na makamashi a duniya da kuma jiragen ruwa na dakon main a kasa da kasa.

Shugaba Ruhani ya kara da cewa, duk inda Amurka ta sanya kafa, to tana haifar da matsalar tsaro ne, a daidai lokacin da dakarun Iran din a cewarsa suke kokarin tabbatar da tsaro.

A daya bangare kuma shugaba Rohani, ya ce a shirye su ke a koda yaushe domin kulla zaman lafiya da kasashe makobtan Iran a daidai wannan lokaci mai cike da zaman tankiya, kuma zamu ma iya yi wa makiyanmu a yankin yafiya, a daidai lokacin da Amurka da yahudawan sahayoniya ke neman cin moriyar halin da ake ciki na rarabuwar kai.

 

3843781

 

 

 

 

 

 

captcha