IQNA

21:39 - September 26, 2019
Lambar Labari: 3484089
Wasu daga cikin jam’iyyun siyasa a Sudan sun nuna rashin amincewarsu da yunkurin raba siyasa da  addini.

Shafin yada labaran arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, a jiya gungun jam’iyyun siyasa masu kishin addini a Sudan sun gudanar da taron manema labarai, inda suka ce sun fahimci cewa gwamnatin rikon kwaryar kasar na hankoron ganin ta raba batun siyasa da addini, da kuma yada batun kulla alaka da Isara’ila.

Murtada Al-taum babban sakataren hadakar jam’iyyu masu kishin addini a kasar Sudan ya fadi a wajen taron manema labaran cewa, abin da gwamnatin rikon kwaryar kasar take yi ba abu ne da za su amince da shi ba, domin kuwa sun yi wa gwamnatin da ta gabata bore ne saboda gazawa wajen kyautata rayuwar jama’a, ba domin tana danganta kanta da addini ba.

Ya ci gaba da cewa za su kafa katangar karfe domin hana wanann yunkuri na gwamnatin hadin kan kasar da aka kafa, kamar yadda kuma ba su taba amincewa da take-taken gwamnatin ban a neman kulla alaka da Isra’ila domin kyautata wa wasu kasashen ketare.

Muhammad Abdulkarim shugaban jam’iyyar Nusratu Shari’a a kasar Sudan ya bayyana cewa yana goyon bayan matakin na hadin gwiwar jam’iyyu masu kishin addini a Sudan, domin kuwa kasar Sudan kasa ta musulmi wadda ta ginu a kan addini, saboda haka ba za su bari a raba addini da harkokin tafiyar da kasa ba.

 

3844778

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: