IQNA

Muhammad Bin Salman A Karon Farko Ya Amince da Hannusa A Kisan Khashoggi

21:46 - September 26, 2019
Lambar Labari: 3484090
Bangaren kasa da kasa, a karon farko yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman ya amince da cewa da hannunsa a kisan Khashoggi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, rahotanni sun bayyana cewa yarima mai jiran gado na Saudiya mohamamd Bin slam ya dauki alhakin kashe fitaccen dan jaridar nan na kasar Jamal Khashoggi a shekara da ta wuce, domin an aiwatar da kisan ne karkashin kulawarsa a cewar sa,

Mohammad bin salam yaki yace komai a bayyanar jama’a game da kisan da aka yi wa kashogin a ofishin jakadancin kasar saudiya dake birnin Istanbul , sai dai hukumar liken Asiri ta Amurka CIA da wasu gwamnatocin kasahen Turai sun bayyana bin Salman a matsayin wanda ya bada umarnin aiwatar da kisan, ko da yake wasu jam’an kasar ta saudiya sun kore hannun kasar game da kisan na Kashoggi.

An gurfanar da wasu yan kasar saudiya guda 11 a gaban koto domin yi musu shari’a kan zarginsu da hannu wajen kisan , daga bisani majalisar dinkin duniya ta fitar da wani rahoto da aciki ta bukaci a gudanar da bincike kan yarima mai jiran gado na Saudiya da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar ta saudiya.

Shi dai kashoggi an ga shigarsa ofishin jakadancin kasar saudiya a birnin Istanbul a ranar 2 ga watan Oktoba, idan yaje neman wata takarda gab da lokacin bukin aurensa, rahotanni sun bayyana cewa an yi gunduwa gunduwa da jikinsa kana aka fitar dashi daga ofishin jakadancin wanda har yanzu baa san inda gawarsa take ba.

3845067

 

 

captcha