IQNA

23:47 - September 30, 2019
1
Lambar Labari: 3484103
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azahar ta samar da sabbin hanyoyi na koyon karatun kur'ani mai tsarki na zamani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyar Azhar ta bayar da bayani kan samar da wani sabon tsari wanda zai taimaka ma masu koyon karatun kur’ani.

Wannan tsari dai an samar da shi ne ta hanyar na’ura mai kwakwalwa, wanda yake dauke da wasu tsare-tsare da mai son koyon kur’ani zai iya binsu domin koyon karatu cikin sauki.

Baya ga haka kuma wanda yake son yin hardar kur’ani cikin sauki zai iya yin amfani da wannan tsari domin kuwa akwai hanyoyi masu sauki da aka tsara a cikinsa, wanda mutum zai iya hardace kur’ani cikin kankanin lokaci idan ya yi amfani da tsarin.

Sayyid Mahmud salim daya daga cikin wadanda suka shirya wannan tsari ya bayyana cewa, an yi amfani da fasaha ta zamani ta na’ura mai kwakwalwa wajen samar da wannan hanya, akmar yadda kuma a cikin akwai makaranta kur’ani da salo daban-daban, baya ga matanin da kuma yadda aka raraba matanin domin karatu ko harda.

Haka nan kuma an samar da application wanda za a iya yin amfani da shi ta hanyoyi na wayar salula cikin sauki.

 

3845969

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
NURA MUHAMMAD
0
0
wannan tsari yayi kyau sosai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: