IQNA

Ayyukan Bankin Muslunci A Habasha

23:00 - October 21, 2019
Lambar Labari: 3484177
Bangaren kasa da kasa, bankin muslunci Zemzem a Habasha ya bude asusu day a kai bir miliyan 600 a cikin ‘yan watanni.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bayan ‘yan watanni da bankin muslucni na zemzem a kasar Habasha ya bude asusun ajiya ga mutane da kudinsu suka kai bir miliyan 600, wanda kuma kaddarorin kamfanin a yanzu sun kai bir biliyan 1.2.

Wannan bankin dai ya samu izini ne bayan sanarwar da firayi ministan kasar ta Habasha Abi Amad ya bayar, na bayar da lasisi ga bankunan musulucni da suke bukatar buda rassa a kasar Habasha.

Tun a  cikin shekara ta 2011 aka bayar da dama ga bankunan Habasha kan cewa suna iya yin mu’amalar kudi ba tare da riba ba idan syuna bukatar hakan, amma ba a yarda su yi tsari irin na muslunci ba.

Akwai bankuna 16 a kasar Habasha na gwamnati, da kuma wasu biyu da ba na gwamnati ba. A cikin 2018 an bayar da saarwar cewa hannayen jarin bankunan kasar ya karu da 10%, inda jimillar kudin bankunan kasar Habasha ya kai dalar Amurka biliyan 85.8, wanda hakan ba su dammar kara yawan basussukan da suke bayar wa ga mutanen kasar.

3851276

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، mutane ، Habasha ، Abi Ahmad
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha