IQNA

An Saka Wa Gasar Kur’ani Ta Duniya A Masar Taken Abdulbasit Abdulsamad

22:54 - October 23, 2019
Lambar Labari: 3484182
Bangaren kasa da kasa, Rahotani daga masar sun ce an sakawa gasar kur’ani ta duniya a Masar taken Abdulbasit Abdulsamad.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin Alwatan News cewa, ma’aikatar kula da harkokin addinia  kasar Masar ta sanar da cewa an sakawa gasar kur’ani ta duniya a Masar sunan Abdulbasit Abdulsamad, sakamakon irin gagarumar hidimar da marigayin ya bayar a duniya wajen hidima ga alkur’ani mai tsarki, wanda za a gudanar da gasar karo na ashirin da bakawai ne a cikin watan Fabrairun 2020.

Shugaban kasar Masar abdulfattah Sisi ne da kansa zai girmama wadanda suka nuna kwazo a  gasar a daren 27 ga watan Ramadan mai zuwa.

 

3851893

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha