IQNA

23:00 - November 05, 2019
Lambar Labari: 3484224
Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya bayyana cewa, a gobe Laraba Iran za ta shiga mataki na hudu na jingine yin aiki da wani bangare na yarjejeniyar nukiliya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaba Rauhani ya fadi yau Talata cewa, bisa la’akari da cewa sauran kasashen da suka cimma yarjejeniyar nukiliya da suka yi saura a cikin yarjejeniyar ba su cika alkawullan da suka daukar wa Iran ba, ya zama wajibi Iran da shiga mataki na hudu na jingine yin aiki da wani bangaren yarjejeniyar, wanda zai fara daga gobe Laraba.

Ya ce za a fara tura iskar gas a cikin bututai 1000 a cibiyar nukiliya ta Fordo, kuma za a fara aikin ne bisa sanya ido na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, kamar yadda aka yi sauran a lokutan baya.

Rauhani ya ce wannan matakin za a iya janye shi idan har sauran kasashen da suke cikin yarjejeniyar suka cika alkawullansu, kamar yadda sauran matakai uku da aka dauka a baya ma za a iya dakatar da su a bisa wannan sharadi.

Ya kara da cewa akwai kasashen da suka tattauna da Iran kan wannan batu wanda har zuwa daren jiya Talata ba a cimma matsaya da ta gamsar da Iran ba, a kan haka babu abin da ya rage illa daukar mataki na gaba.

A cikin yarjejeniyar nukiliyar dai an ambaci cewa Iran za ta iya yin watsi da wani bangaren yarjejeniyar idan har aka samu wata kasa daga cikin kasashe da suka rattaba hannu a kanta ba ta yi aiki da ita, wanda hakan hakki ne na Iran a matsayin martani.

Iran dai ta dauki wannan matki ne bayan da Amurka ta sanya kafa ta yi fatali da wanna yarjejeniya wadda ta rattaba hannu a kanta tare da sauran manyan kasashe.

3854934

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: