IQNA

23:47 - November 08, 2019
Lambar Labari: 3484234
Bangaren kasa da kasa, Ayatollah Sistani ya ce hakkin mutanen Iraki ne su yi jerin gwano na lumana domin bayyana korafinsu.

kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da hudubar Juma’a a jiya a Karbala, wakilin Ayatollah Sistani Sheikh Mahdi Karbala’i ya bayyana cewa, matsayar Ayatollah Sistani ita ce kowane dan kasa yana hakkin gudanar da jerin gwano na lumana, domin kokawa kan matsalolin al’umma.

Ya ce dole ne jam’iyyun siyasa da suke mulki su mayar da hankali wajen saurarre bukatun jama’a da kuma gaggauta daukar matakai na warware abubuwan da jama’a suke korafia  aknsua  kasar.

Wakilin Ayatollah Sistani ya ce, a lokaci guda kuma suna jan hankali ga al’umma da su zama  cikin fadaka, domin kada su aiwatar da duk wani abin da zai cutar da kasarsu ko rusa ta, ta hanyar karkata akalar bukatunsu zuwa wasu abubuwa na daban, wadanda za su jefa kasar cikin wani mawuyacin hali.

Domin kuwa jerin gwano da ban a lumana bai halasta ba, kuma zai cutar da kasa da al’ummarta.

Haka nan kuma ya ja hankulan masu zanga-zanga da su nianta kansu daga wadanda suka cutar da Iraki tsawon shekaru, wadanda suke son su yi amfani da wannan damar a halin yanzu domin daukar fansa kan al’ummar kasar, da kuma juya manufar zanga-zangar daga neman gyara zuwa barna.

Kamar yadda kuma ya bayyana cewa bai kamata a manta da irin sadaukarwar da dakarun kasar gami da dakarun sa kai suka yi wajen ‘yantar da kasar daga mamayar ‘yan ta’addan Daesh ba.

 

 

3855447

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: