IQNA

15:51 - November 21, 2019
Lambar Labari: 3484263
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara zaman taro na duniya kan gyaran masalatai a birnin Kualalmpur na kasar Malaysia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cwa, a cikin mako mai zuwa ne za a fara zaman taro na duniya kan gyaran masalatai a birnin Kualalmpur na kasar Malaysia.

Saudiyya da Malaysia ne za su dauki nauyin gudanar da zaman taron.

Manufar taron dai ita ce samar hanyoyi na wayar da kan gwamnatoci da kumacibiyoyin musulmi kan gyaran masallatai a duniya.

Za a gudanar da taron ne daga ranar 25 zuwa 27 ga wanna wata na Nuwamba, wanda mutane 9 za su gabatar da jawabai, yayin masana 45 daga kasashe daban-zasu gabatar da makaloli da suka rubuta kan batun, kuma za a zabi makalar da tafi domin bayar da kyauta ga wanda ya rubuta ta.

3858285

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، rubuta ، Nuwamba ، Malaysia ، masallatai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: