IQNA

18:42 - December 01, 2019
Lambar Labari: 3484284
Wani dan kasuwa dan kasar Pakistan zai dasa itatuwa kan hanyar masu ziyarar arba’in daga Najaf zuwa Karbala.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Muhammadi Darbar wani dan kasuwa ne kuma dan asalin kasar Pakistan, wanda ya sha alwashin dasa itatuwa kan hanyar Najaf zuwa Karbala domin amfanin masu ziyarar arba’in.

Ya ce bayan dawowar matasarsa da jikansa daga ziyarar arba’in ya ga cewa fusakunsu sun duhu, daga nan ya gane cewa lallai akwai zafi a kan wannan hanaya.

A kan haka ya ce ya kudiri  aniyar dasa itatuwa masu inuwa a kan hanyar Najaf zuwa Karbala domin masu ziyarar su rika tsayawa suna shan inuwa suna hutawa.

Haka nan uma ya bayyana cewa sun tattauna da jami’an gwamnatin Iraki kan batun kuma sun amince, inda a halin yanzu tuni injiniyoyi suka isa suka duba hanyar kuma suka bayar da rahoton cewa aikin zai yiwu.

Ya ce yanzu haka an aike da kawunan itace dubu 9 da dari takwas wadanda za a fara dasawa, wadanda suka kunshi nau’in itatuwa takawas.

3860847

 

https://iqna.ir/fa/news/3860847

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، pakistan ، Najaf ، Karbala
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: