IQNA

22:51 - December 02, 2019
Lambar Labari: 3484288
Bangaren kasa da kasa, Majalisar dokokin kasar Iraki ta amince da marabus din da firayi ministan kasar ya gabatar mata.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, wasu rahotanni sun bayyana cewa majalasar dokokin kasar Iraki sun amince da takardar murabus da fira ministan kasar Adil Abdul Mahdi ya mika mata.

Wannan ya zo ne bayan da babban malamin shia’a a kasar Ayatullah SIstani ya yi kira ga ‘yan majalisar da su sauya nuna goyon bayansu ga gwamnatin. Sai dai ana sa ran gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har sai an amince da sabon dan takarar da zai maye gurbinsa.

Tuni dai kakakin majalisar dokokin kasar Mohammad Al-Halbusi ya bukaci shugaban kasar Barham Salih ya jagoranci fitar da dan takarar da za’a saba a matsayin sabon fira ministan kasar.

Tun a ranar juma’a da ta gabatana ce Abdul Mahdi ya sanar da cewa zai mika takardar yin murabus dinsa ga majalisar domin amsa kiran da babban malamin shia’a a kasar Ayatullah sisitanni ya yi na daukar matakin da ya dace game da makomar kasar.

 

3860951

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: